Bismillahi Rahamani Raheem,

Godiya ta tabbata ga Allah SWT shi kadai daya hallichemu Musulmi, ya kuma bamu ikon bautamasa. Allah yayi dadin tsira ga Annabi Muhammad SAW. A wannan rana ta laraba 1 ga watan shawwal, da muke bukin Sallah wanda ya kawo karshen wata mai daraja na Ramadan.

Yan uwa Musulmi ina gargadinmu damu natsu da neman ilmi ta kowanne hali kamar yadda Allah SWT ya umarchemu. Ita ibada bata karbuwa a wajen Allah, saida imani da kuma sanin yadda Annabinmu Muhammad SAW ya koyar damu cikin litafin Allah Kurani da kuma ingantatun hadisai.

Ta hanyar sanin tauheed da hukunce hukuncen sanema zamu san hakkin kanmu, na iyayenmu, na matanmu da mazajenmu, na yayanmu da yan uwanmu na kusa, na makwabtanmu dana abokan hurdarmu, na alumarmarmu dana abokan zamanmu wadanda ba musulmi ba.

Hanyar tsira a garemu guda dayace ta hanyar sanin tauheed da kuma aiki da shi. Idan mun kiyaye da dokokin Allah SWT, shi zai kiyayemu daga manyan zunubbai, kamar su shirka, kisankai bata hanyar sharia ba, tsubbace tsubbace da bokanci,, zina da luwadi da danne hakkin marasa karfi, shangiya, chacha, ribah, rashin daa ga iyaye, rashin biyan zakkat, karya alkawari, karya, cin hanchi da rashawa, cinye kudaden hukuma bata yadda doka ta shimfida ba, baza jita jita, tsegumi da annamimanchi, da makamantan wadannan. kuma ya yafemana kananan kusakurenmu.

Muna rokon Allah ya kiyayemu damu da yayanmu daga manyan zunbbai, Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya a gidajenmu, garuruwanmu, jiharmu da kasarmu. Allah ya gyara zukatun shugabbanninmu, Allah bamu ikon gane gaskiya kuma muyi aiki da ita, kuma mu gane karya mu nisanta da ita. Muna rokon Allah ya karbi ibadojinmu na baya da wanda zamuyi a nan gaba. Allah ya maida kwa gida lafiya. Inayimuku barka da Sallah.