GABATAR DA RABON ZAKKAH NA MASARAUTAR DUTSE KARSHEN SHEKARAR1425AH A GARIN DANFUSAN GUNDUMAR KIYAWA
Da sunan Allah mai Rahama mai Jinkai, Muna salati ga Annabi Muhammadu SAW
Da alayensa da sahabbansa.
Shika-shikan Musilumchi guda biyar, Tawhidi,Sallah,Zakkah,Azumi da Hajji in an hadasu da muamaloli, kamar neman Ilmi, Aure, zartar da cinikayya, kyautatawa iyaye da matan Aure, yaya da yanuwa, da makwabta nesa da kusa sune musulimchi.
Tauhidi shine sanin abubuwan da suka kebanta ga Allah Taala, shine kadai ke hallita, da kuma chanchantar a bautawa. Tauhidi yana da fuska uku. Fuskar da ake iya gain shine fadin kalmar shahada. Fadin “Babu wanda ya canchanta a bauta masa da gaskiya sai Allah Taala. Ya aiko Annabi Muhammadu SAW ya bayyanawa mutane yadda akeyin bautar Allah.
Fuska ta biyu, itace yarda da cewa Allah Taala bashi da farko bashi da karshe. Kuma da yarda da littafansa, Samuwar Annabawa da manzonni wanda suke bayyana dokokin Allah. Da kuma yarda da ranar tashin kiyama.
Fuska ta uku, itace koyi da aiki da abinda Annabi ya kawo mana da niyyar bautawa Allah shi kadai, ba kirkire kirkire domin neman gwaninta ko yardarm wani mutum.
Abinda ya taramu anan a yau shine daya daga cikin shikashikan musilinchi wan da byan Sallah sai shi a muhimamchi itace ZAKKAH.
Ita Zakkah ana bayar da ita ga FAKIRI wato mai wani abu amma bazai iya biyan bukatunsa na rayuwaba. MUSAKI wanda bashi da cin yaau balle na gobe. MAI AIKIN TARA ZAKKAH. Kafirin da ake kwadaitawa addinin musilimchi. BAWA da yake neman fansar kansa. MATAFIYI wand guzirinsa yakare a halin tafiya. Da kuma MALAMAI masu koyarwa ko waazi, ko masu yakin jihadi domin daukaka kalmar Allah.
ABUBUWAN DA AKE FITAR DA ZAKKAH A WANNAN MASARAUTA SUNE
1. Daga amfanin gona, Gero, Dawa, Alkama, Shinkafa, Ridi, Gyada, Wake, da Dabino. Nissabin ko wane daga cikinsu shine WUSQI biyar wato SA’I 300 ko mudannabi 1200. Ana karbar wannan Zakkar sau daya a shekara bayan girbi, wato kashi daya daga cikin goma na abinda aka girba idan noman ruwan samane. Idan kuma na noman ranine kashi daya daga cikin ashirin na abinda aka girba.
2. Daga Dabbobi Shanu idan sunkai 30, Awaki da Tumakai idan sun kai 40.
3. Zinariya da Azurfa wanda ya mallaki zinariya 20 ko dirhami 200 suka shekara a gunsa zai bada Zakkar kashi daya daga kashi arbain.
4. Kudinmu na Naira a wannan shekara idan sun kai Nisabin N155,170. wato daidai da zinariya 20 mai nauyin oz 2.7328.
ABINLURA A SHEKARAR DA MUKE CIKI
1. Diyyar Rai a Kuskure zinare 1000 ko nauyin oz 136.364 ko Naira 7,758,095
2. Sadakin Aure ko mace ko budurwa babu banbanci mafi karanchin kudi shine Naira 1,940.
A bias wannnan ina jawo hankalin Malamai da su tabbatar sun kare dokokin Allah musamman wajen bayar da Sadaki.
Wassalam,
DUTSE ZAKKAT MONETARY COLLECTION AND EXPENDITURES 1425 AH
CASH VALUE OF DUTSE EMIRATE ZAKKAT TOTAL COLLECTIONS FOR THE YEAR 1425 AH
|