Tabbatarwa da Mai Girma MUHAMMAD HAMIM NUHU SANUSI a MATSAYIN SABON SARKIN DUTSE NA (20)

Amincin Allah ya Tabbata a gareku tare da Iyalan ku.
Lahadi, 05/02/2022.

Muna Masu Sanar da Jama’a Cewa Gwamnatin Jihar Jigawa a Karkashin Jagorancin Mai Girma Gamna Muhammad Badaru Abubakar MON, Mni ya Tabbatarwa da Mai Girma MUHAMMAD HAMIM NUHU SANUSI a MATSAYIN SABON SARKIN DUTSE NA (20).

Muna kara Gayyatar Daukacin Jama’ah dasu fito kwansu da kwakwata su domin taryen Mai Martaba Sabon Sarki a Filin Tashi n Jirage da Sauka a na Masarautar Dutse da Misalin karfe 2:30 na yau dinnan.


Allah ya jiƙan Sarki, Allah yasa yana cikin Dausayin Aljannah Firdausi. Allah ya taya riko, Allah ya riko da hannayensa. Ameen.

 

✍️: WAZIRIN TAFARKIN DUTSE
Fadar Mai Martaba Sarki